Rubutu na asali a Turanci ta Tactical Tech, fassarorin & daidaitawa ta abokan tarayya:
A cikin wannan darasin, zaka maida hankali kan bayanan bogi-yadda suke, yadda ake yadasu, da yadda zaka iya magance su, zaka koyi tsarin yadda ake kiyaye labaran bogi. Za kuma kalli yadda ake amfani da fasahar zamani wajen canza yanda kake ji, gani, imani, da abubuwan da zaka iyayi game da su.
Ƙarfafa kanka- samar da fahimta akan bincike, sanin yadda ake wallafa bayanin binciken, kiyaye sharadin “Ba cuta ba cutarwa”, da kuma sanin yadda zaka kiyaye kai da sauran al’umma.
Koyon yadda zaka gane ire-iren labaran bogi da irin tasirin hadarin da suke haifarwa.
Fahimtar dalilin da yasa aka zabi labaranka, tare da sanin yadda ko ya dace kayi imani da bayanan.
Koya tare da gane labarai marasa tushe, gane adireshin yanar gizon ‘yan zambo, sannan da fahimtar yadda tsarin masu bibiya yake.
Gano yadda zaka fahimci yan shigo-shigo ba zurfi, domin sun iya kwaikwayo da tsara labarai.
Amsa wadannan tambayoyin don bitar abubuwan da aka koya cikin wannan darasi na farko na kundin binciken fasaha.